’Yan bindiga a Zamfara sun kai farmaki garin Dansadau don nuna fushinsu kan sauke basaraken garin, Alhaji Hussaini Umar, da gwamnatin Jihar ta yi.
Sanata Sa’idu Muhammad Dansadau ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa ’yan bindigar sun sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a garin Dansadau har sai hukumomin jihar sun mayar da sarkin kan kujerarsa.
- Makabartar Gombe da ake binne akalla jarirai 10 a kullum
- Mutum 3 sun mutu bayan ambaliya ta shafe hanyar Bauchi zuwa Kano
“’Yan bindigar suna shaida wa wadanda suka sace cewa garin Dansadau ba zai san zaman lafiya ba har sai an mayar da sarkin kan karagar mulki; wannan ya nuna karara cewa matakin da hukumomi suka dauka na tsige sarkin ya yi daidai.
“Sarkin yana da hannu a ayyukan ’yan bindigar da barayin shanu, in ba haka ba me zai sa su yi adawa da tsige shi. Wannan ya tabbatar yana da alaka da su sosai.
“Ya kamata kwamitin da aka dora wa alhakin binciken sarkin ya gaggauta daukar mataki tare da mika rahotonsa ga hukumomi.
“Yanzu haka sarkin na tsare, wayoyinsa da kayan aikin ofisoshinsa duk gwamnati ta kwace. Bai kamata gwamnati ta biye wa wadannan miyagun mutane ba,” inji Sanata Dansadau, wanda ya wakilci mazabar Zamfara ta Tsakiya daga 1999 zuwa 2007.
A watan Yunin wannan shekarar ne Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya sanar da tumbuke sarkin bisa zargin alaka da ’yan bindiga, sannan ya kafa kwamiti karkashin jagorancin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, DIG Ibrahim Mamman Tsafe, don gudanar da bincike kan sarkin.