’Yan bindiga sun kashe jami’in dan sanda suka kuma yi garkuwa da wasu ’yan sandan a Jihar Imo.
Maharan da ake zargin ’yan fashi ne sun sassari wani dan sandan mai mukamin Sajan da adduna suka kuma dauke bindigarsa a garin Nkwerre.
Sun kuma yi awon gaba da jami’an ’yan sanda da ba a kai ga tantance yawansu ba bayan sun kona motocin sintitin da ’yan sandan.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata a Karamar Hukumar Nkwerre ta jihar ta Imo.
An garzaya da dan sandan da ya samu raunuka zuwa asibiti a garin Orlu, inda daga baya ya ce ga garinku.
A garin Egbu ma wasu ’yan bindidga sun yi wa ’yan sanda kwanton bauna, suka kwace bindigar wani jami’i suka kuma raunata wani da sarar adda.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Imo Iassac Akinmoyede ya tabbatar da aukuwar hakan, ya kuma ce suna bin sahun bata-garin.