’Yan bindiga sun hallaka mutum biyu tare da garkuwa da wasu mutum 48 a kauyukan Karamar Hukumar Batsari ta Jihar katsina
Wani mai rike da sarauta ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindiga sun kashe mutum biyu a kauyen Daurawa inda suka kuma yi garkuwa da wasu biyar a ranar Juma’a da dare.
- An cafke basarake a cikin ’yan bindiga a Neja
- ’Yar Shaikh Ibrahim Nyass ta rasu
- Gawuna ya wakilci gwamnatin Kano wurin yi wa Kwankwaso ta’aziyya
Da misalin karfe bakwai na daren ranar Asabar kuma ’yan bindiga suka kai wa kauyen Garin Dodo hari, inda suka yi awon gaba da mutum 32, inji wata majiya.
“Mutum biyu daga cikin wadana da aka yi garkuwa da su sun samu tsarewa ragowar 30 kuma na hannun maharan,” inji ta.
Mahara sun kuma yi garkuwa da mata 10 a kauyan Biya Ka Kwana, inda suka harbi wani mutum da yanzu yake jinyan shi a Asibitin Batsari.
Majiyar Aminiya ta ce a ranar Asabar da dare an dauke mutum biyar a harin da aka kai kauyen Watangadiya, Karamar Hukumar ta Batsari.
Masu garkuwa sun kuma yi wa Tudun Modi da ke Karamar Hukuma dirar mikiya suka dauke mutum uku, tare da harbin wani karamin yaro da ke samun kulawa a asibiti.
Shin an kawo dauki?
Aminiya ta nemi jin ta bakin mazauna kauyukan ko sun samu dauki daga jami’an tsaro a lokacin da aka kai musu hare-haren.
Mazauna sun ce, “’Yan sanda suna iya bakin kokarinsu amma da alama ’yan bindigar sun fi karfinsu.
“Maharan sun bullo ne ta Gabas da Yamma da Kudu da Arewa, jami’an tsaron da ke nan kuma ba su da yawan da za su iya tunkarar su cikin a dan kankane lokaci,” inji su.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa, bai kai ga tabbatar mana da abin da ya faru ba, inda ya ce yana jiran karin bayani daga Babban Baturen ’Yan Sandan yankin.
Ba yanzu farau ba
Jihar Katsina na yawan fama da ayyukan ’yan bindaga wadanda a baya-bayan nan suka sace dalibai 344 a Makarantar Sakandaren GSSS a garin Kankara, lamarin da ya sha la’anta da kiraye-kirayen a sako yaran.
Sakin daliban ke da wuya kuam ’yan bindiga suka yi awon gaba da daliban Islamiyya 80 a garin Mahuta na Karamar Hukumar Dandume, amma sojoji suka ceto su.