✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 40 a Taraba

’Yan bindiga sun sace mutane 40 a Karamar Hukumar Bali ta Jihar Taraba

’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane akalla 40 a Karamar Hukumar Bali ta Jihar Taraba, inda bata-garin suka kai wa hare-hare a kauyuka.

Al’ummomin yankin da aka kai harin sun ce ’yan bindiga kusan 200 a kan babura ne suka far wa kauyukansu suka rika garkuwa da mata da kananan yara da maza da shanu zuwa cikin daji, wanda hakan ya sa mazauna yankunan tserewa.

Wasu daga cikinsu da suka tsere zuwa garin Garba-Chede sun shaida wa wakilinmu cewa kauyuka 15 ne dandazon ’yan bindigan suka tsarwatsa, saboda irin “muggan makaman da ke hannunsu.”

Wani mazaunin garin Garba-Chede mai suna Ali Dauda ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa daruruwan ’yan gudun hijira daga kauyukan da  ’yan bindiga suka kai wa harin na ta gudowa zuwa garinsu.

A cewarsa, jami’an tsaro ba su kai ga zuwa yankin ba, amma mafarauta da ’yan banga sun kai dauki domin tunkarar maharan.

Aminiya ta gano cewa kauyukan da aka kai wa harin sun hada da Garbatau da  Mirimidankol da Gidan Hamidu da Dangiwa da kuma Nayinawa da Garin Gima da Bantaguru da ShaDussa da Garin Bose.

Sauran sun hada da da Mailabari da dai sauransu, inda mazaunansu suke tsere zuwa Garba Chede da Sunkani da kuma garin Jalingo, babban birnin jihar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Usman Abdullahi ya tabbattar da harin, amma ya ce mutum 14  suka samu labarin an yi garkuwa da su.