Wasu ’yan bindiga da suka farmaki yankin Kiyi da ke Kuje a Abuja tare da garkuwa da mutum hudu.
Wata majiya a yankin ta ce maharan sun sace wani ma’aikacin Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya (FCTA) da wasu mutum uku.
- An kwace mota 10 ta gurbataccen sigari a Kano
- An kama matar da ta kashe kishiyarta ta kona gawar
- Ma’aikatan jaridar Gaskiya 100 sun mutu suna jiran hakkokinsu
- Dalilin da ba za a yi ‘zaben Kananan Hukumomi ba’ a Filato
Dan uwan daya daga wanda aka yi garkuwa da su ya ce, “Masu garkuwar sun kira mu a waya, suna bukatar N50m kan kowane mutum”.
Kudin fansar mutanen da aka sace baki daya ya kama N200m.
Ragowar mutane ukun da aka yi garkuwa da su hadar da wani direban tasi, dan acaba da kuma wani daban.
Aminiya, ta gano yadda ’yan bindigar suka shiga gidan daya daga cikin mutanen ta taga, tare da yin awon gaba da shi zuwa cikin daji.
Da muka tuntubi kakakin ’yan sandan birnin tarayya, Abuja, ASP Miriam Yusuf, ta tabbatar da sace mutanen, inda ta ce Rundunar na kokarin ceto su.