‘Yan bindiga sun yi garkwa da akalla mutum 10 a wani hari da suka kai a kauyen Tungar-Maji da ke makwabtaka da birnin Abuja.
Mazauna sun ce maharan da suka kai harin da safiyar Alhamis sun yi awon gaba da adadin mutane da ba a kai ga tantancewa ba, amma wasu na ganin adadin ya kai mutum 20.
“Ba mu yi barci ba da dare. Da safe ne ‘yan banga suka ce an yi garkuwa da kuma mutum 20″, inji wani mazaunin garin na Tungar Maje.
Shi ma wani mazaunin garin da ya bukaci a sakaya sunasa ya ce maharan su kusan 20 sun far wa ganin ne da tsakar inda suka yi ta bin wasu gidaje masu kallon wata makarantar sakandare inda suka yi awon gaba da mutanen.
Jaridar Premium Time ta ruwaito wani mazaunin yankin da ke cewa maharan sun kutsa ne da tsakar dare inda suka yi ta harbe-harbe na kimanin awa daya lamarin da ya gagari ‘yan banga.
Wata majiyar tasro ta shaida wa wakilinmu cewa bayan harin, ‘yan bindigar sun shige dajin Shenagu inda ake zargin maboyarsu take da misalin karfe 4 na asuba.
Wata majiya ta ce ‘yan sanda daga Zuba sun yi arangama da maharan, wadanda Babban Jami’in Ofishin Zuba ya ce an kwato yara uku da wani tsoho da kuma mata mai ciki a hannunsu.
Ya ce maharan da ke tafe a kasa, sun tsere ne bayan isowar ‘yan sanda da suak yi nasarar kwato mutum biyar din da aka garzaya asibiti da mutum biyu da ga cikinsu.
Jami’in ya ce suna ci gaba da aiki domin ganin an kwato sauran wadanda aka yi garkuwan da su.
Harin na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan rahoton hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce mayakan Boko Haram sun kafa sansanoni da nufin kai hare-hare a wasu wurare a Abuja.
Daga baya Rundunar tsaro ta Najeriya ta ce, ta riga ta sha gaban masu nufin kai harin, ta kuma ba wa mazauna tabbacin babu wani abin tsoro.