✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da lauyoyi 2 a Ribas

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da lauyoyi biyu a hanyar Iloabuchi zuwa unguwar Mile 1 Diobu, da ke Fatakwal jihar Ribas. Wanda aka yi…

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da lauyoyi biyu a hanyar Iloabuchi zuwa unguwar Mile 1 Diobu, da ke Fatakwal jihar Ribas.

Wanda aka yi garkuwan da su, su ne: Barista John Joseph shugaban jam’iyyar APC na mazabar Ward 8 a karamar hukumar Emohua da Barista Stephenson.

An dai yi garkuwa da su ne a jiya Lahadi, bayan su na hanyarsu ta dawo daga taron siyasa da jam’iyyar su APC ta shirya a harabar rukunin gidajen gwamnati da ke babban birnin jihar.