Shugaba Tinubu ya haramta sayen motoci masu amfani da man fetur a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Najeriya.
Shugaban kasar ya kuma umarci motocin su koma amfani da ababen hawa masu amfani da iskar gas.
A jawabinsa ga Majalisar Zartaswa ta Kasa, Shugaba Tinubu, ya ce babu gudu babu ja da baya kan batun komawa amfani da ababen hawa masu amfani da iskar gas a Najeriya.
A cewarsa, hakan na daga cikin matakan da gwamnatinsa ta dauka na tabbatar da wadataccen makamashi da kuma rage tsadarsa a kasar.
Ya kuma ba da umarnin soke duk takardun bukatar sayen ababen hawa masu amfani da fetur da mambobin majalisar suka gabatar, yana mai umartar su da su je su mayar da takardun na neman sayen masu amfani da iskar gas.
Shugaban kasan ya bayyana cewa umarnin daga cikin matakan gwamnatinsa na tabbatar da amfani da makamashi mara gurbata muhalli, lura da cewa motoci masu amfani da iskar gas ba sa fitar da hayaki.
Hakazalika ya ce ababen hawa masu amfani da iskar gas sun fi saukin kudi, da yiwuwar sauƙin samu ga ’yan Najeriya.
A kwanakin baya ne dai Ministan Kudi, Wale Edun ya yi rangadin masana’antar kera ababen hawa masu amfani da iskar wadanda ya ce nan gaba kadan za a kaddamar da su domin amfanin ’yan Najeriya.