Wasu ’yan bindiga da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun sace lakcara biyu a Jami’ar Jihar Abiya a yammacin ranar Alhamis a kan titin ABSU zuwa Isuikwuato, a Umuahia babban birnin jihar.
Farfesoshin da aka yi wa fashi sannan aka yi garkuwa da su na koyarwa ne a Sashen Kimiyyar Masana’antu da kuma Sashen Sadarwa na Jami’ar Abiya.
- Gwamnatin Gombe al’ummar Gabukka na neman dauki
- Hakeem Baba-Ahmed: Kakakin Dattawan Arewa ya koma PRP
Shugaban Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) Reshen Jami’ar Abiya, Uturu V. U. Nkrmdirim, ya tabbatar da faruwar lamarin a misalin karfe 6 na yammacin ranar Alhamis.
Ya bayyana cewar malaman jami’ar na kan hanyarsu ta yin tafiya ne lokacin da suka yi kicibus da ’yan bindigar da suka yi garkuwa da su.
Sai dai an tsinci motar daya daga cikin lakcarorin kirar Toyota Camry da wayarsa a wurin da aka sace su.
Nkrmdirim ya kara da cewar iyalan malaman sun tabbatar da sace su kuma ASUU na bibiyar lamarin.
Ya zuwa yanzu dai wadanda suka yi garkuwa da malaman jami’ar ba su kira ko nemi iyalan lakcarorin ba.