✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da direba da fasinja 16 a Jihar Ribas

A makon jiya ne wasu ’yan bindiga da ba a tantance ko su waye ba suka kama wata motar fasinja dauke da fasinja 16, suka…

A makon jiya ne wasu ’yan bindiga da ba a tantance ko su waye ba suka kama wata motar fasinja dauke da fasinja 16, suka yi garkuwa da su a garin Fatakwal, Jihar Ribas.

Kamar yadda Aminiya ta samu labari, al’amarin ya afku ne a yankin Emohua, daidai mahadar babbar hanyar nan ta East-West da ke Fatakwal. Al’amarin ya faru ne, kamar yadda wani ganau da ya bukaci a boye sunansa ya ce; motar ta taso ne daga tashar da aka yi mata lodi za ta kama hanyarta zuwa Legas sai wasu ’yan bindigar suka datse hanyar; motar tana na zuwa wurin da suke sai suka bude mata wuta, suna ta harbin kan mai uwa da wabi. Ganin haka ya sanya dole direban motar ya taka burki ya tsaya, domin tsira da ransa da kuma na fasinjojin da ke cikin motar. Daga nan ne maharan suka karkata akalar direba da motar da kuma ilahirin fasinjojin cikinta zuwa wani kurmi.

Aminiya ta tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ribas DSP Nnamdi Omoni game da halin da ake ciki, ya ce: “Hakika hakan ya faru amma bayanan sirri da muke samu daga bakunan wadanda aka yi abin a gabansu, muna bi kuma da zarar mun bara za mu sanar maku.”

Ya kara da cewa wasu ’yan kasa nagari na nan na aiki tare da mu, domin gano maboyar maharan da kuma inda fasinjojin suke, domin a kubutar da su. Wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ribas, Zaki Ahmed ya fitar ta yi nuni da cewa tuni aka tura jami’an tsaro na hadin gwiwa yankin.