Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da dagacin kauyen Mashio da ke Karamar Hukumar Fune ta Jihar Yobe.
A daren Lahadi ne ne maharan da suka razana mazauna da harbe-harbe suka dauke Alhaji Isa Mai Buba Mashio da dansa mai shekara 35.
Wani shaida ya ce daga baya dan basaraken ya tsere amma ya samu raunin bindiga.
Dan Majalisar Dokokin Jihar Yobe mai Wakiltar Mazabar Jajere, Chrioma Buba Mashio ya ce jama’a sun dauka harin Boko Haram ne, kafin daga baya suka fahimci cewa masu garkuwa da mutane ne.
Ya ce ’yan banga da jami’an tsaro na bin sawun maharan tun Asabar da dare.
“Yanzu haka muna cikin daji tare da jami’an tsaro da mafarauta muna bin sawunsu. Muna zargin a kafa suke tafiya domin babu alamar sawun mota, kawo yanzu”, inji shi a zantawarsa da wakilinmu ta waya.
Dan majalisar ya ce maharan sun kira waya suna barazanar kashe basaraken idan ba a daina bin su ba “amma mun yi watsi da su”.
Ya ce yana tuntubar manyan jami’an gwamnati domin ganin an ceto basaraken daga hannun ’yan bindigar.