A daran ranar Asabar ne wasu ’yan bindiga da ba a san adadinsu ba suka kai hari unguwar Kuregu da ke Wusasa a Zariya, inda sukayi awon gaba da mutane shida, cikinsu har da iyalan wani dan sanda kwantar da tarzoma.
Masu garkuwa da mutanen sun far wa unguwar ne a yayin da ake gudanarwa da bikin Kirsimeti.
- COVID-19 ta kama sama da mutum 100,000 a Faransa ranar Kirsimeti
- Yadda rasuwar Desmond Tutu ta girgiza Afirka ta Kudu
Mazauna yakin na Wusasa dai sun saba da irin wadannan farmakin na tsawon lokaci.
Maharan dai sun shiga unguwar ne da misalin karfe 10:30 na dare, ba tare da yin harbi ba.
Bayanan da Aminiya ta samu sun nuni da cewar wadanda aka tafi da su akwai matar wani dan sandar kwantar da tarzoma mai suna Ibrahim Diboga da kuma ’yarsa.
Kazalika, cikin wadanda ’yan bindigar suka tafi da su sun hada da wata mata mai suna Maman-Kyauta, da kuma wani mai suna Joseph, da wani mai sana’ar sai da shayi duk a anguwar.
Bayanan sun kara da cewa a lokacin da suka yi kokarin shiga gida na hudu ne ’yan sintiri na KADVS suka isa Anguwar ta Kuregu, nan da nan suka fara musayar harbi da bindigogi da su.
Sai dai duk da haka, sai da maharan suka tafi da mutanen da suka dauka.
Duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Rundunar ’Yan Sanda Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ta hanyar kiran wayarsa ya ci tura.