✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun yi awon gaba da limaman coci 3 a Kogi

Suna kan hanyarsu ce ta zuwa wa'azi kwana uku lamarin ya rutsa da su

Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da wasu limaman coci su uku a kan hanyar Ochadamu zuwa Ejule da ke Karamar Hukumar Ofu ta Jihar Kogi, inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 80 kafin su sake su.

Aminiya ta gano daya daga cikin malaman da aka sace, Fasto Sunday Emmanuel Abbah dan asalin Karamar Hukumar Olamaboro ne, amma mazaunin Lakwaja, babban birnin Jihar.

Suna dai kan hanyarsu ce daga Lakwaja don halartar wani taron wa’azi na kwana uku a Gabashin Jihar, lokacin da suka ci karo da ’yan ta’addan.

Rahotanni sun ce maharan sun gindaya motarsu ne a kan hanyar, sannan suka kwashe mutanen zuwa cikin daji.

Wata majiya daga daya daga cikin iyalan malaman cocin ta ce masu garkuwar sun kira su a waya, inda suka bukaci a ba su Naira miliyan 80 kafin su sako su.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce tuni ta aike da jami’anta zuwa yankin don ceto mutanen.

A cewar Kakakin Rundunar, SP William Aya, suna nan suna kokarin ganin mutanen sun kubuta.