Wasu ’yan bindiga sun kai hari yankin Mararaba Akunza na Jami’ar Tarayya da ke Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa sannan suka yi awon gaba da mutum hudu.
Ana kyautata zaton dai dukkan mutanen da aka sace daliban makarantar ne.
Aminiya ta gano cewa lamarin ya faru ne tsakanin karfe 7:00 zuwa 8:00 na daren Asabar, lokacin da ake tafka ruwan sama.
Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce gungun ’yan bindigar sun rika harbi a iska kafin su sace mutanen sannan suka tafi da su wurin da ba a kai ga tantancewa ba.
Tuni dai masu garkuwar suka tuntubi iyalan daliban da misalin karfe 11:30 na daren Asabar suna neman a basu Naira miliyan 25 a matsayin kudin fansa.
Majiyar ta ce, “Lokacin da suka zo ranar Asabar ana ruwa ne, inda suka shigo dauke da bindigunsu kirar AK-47, inda suka kwashe sa’o’i suna cin karensu ba babbaka, har suka sami nasarar sace daliban jami’ar su hudu sannan suka tafi da su.”
Wakilinnu ya gano cewa daga cikin daliban da aka sace har da Zafir Yahaya, dan fari ga Yahaya Adams, fitaccen dan siyasa a Jihar wanda aka fi sani da Majo.
To sai dai Kakakin jami’ar, Ibrahim Abubakar, ya musanta cewa mutanen da aka sace dalibansu ne.
Ya ce, “Sam ba dalibanmu ba ne saboda ba mu sami rahoton bacewar ko da mutum daya daga cikinsu ba. Hasali ma ya faru ne a wajen makaranta, kuma har yanzu babu iyayen da suka yi korafin batan ’ya’yansu.”
Shi kuwa kakakin ’yan sandan Jihar, ASP Nansel Ramhan ya ce su ma a kafafen sada zumunta suka ji labarin, kuma har yanzu ba su karbi korafi ba daga makarantar a hukumance.
Amma ya ce tuni suka dukufa wajen ganin sun kubutar da mutanen nan ba da jimawa ba.