Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bai wa Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), umarnin tsare Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.
Mai shari’a Maryanne Aninih, ta umarci EFCC ta tsare Bello a hannunta, tare da sanya ranar 10 ga watan Disamba domin yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa.
- ’Yan daba sun kashe ɗan sanda da duka har lahira a Adamawa
- Lafiyata ƙalau, amma wasu na min fatan mutuwa – Obasanjo
Lauyoyi daga ɓangarorin EFCC da Bello sun yi muhawara kan buƙatar bayar da belinsa.
Lauyan Bello, Joseph Daudu (SAN), ya roƙi kotun ta bayar da belinsa, inda ya ce laifukan da ake tuhumar tsohon gwamnan na cikin waɗanda za a bayar da beli.
Sai dai lauya mai gabatar da ƙara, Kemi Pinheiro (SAN), ya ƙalubalanci buƙatar belin.
Bello, tare da wasu tsoffin jami’an gwamnatin Kogi, Abdulsalami Hudu da Umar Oricha, an zarge su da haɗa kai wajen amfani da kuɗaɗen gwamnati don sayen kadarori a Abuja da Dubai, na kimanin Naira biliyan 110.4.
Kafin fara zaman kotun, an tsaurara tsaro a wajen kotun, inda jami’an sojoji, DSS, EFCC, da ‘yan sanda suka yi dafifi.
Bello ya shiga ɗakin kotun sanye da farar babbar riga da hula mai launin shuɗi mai haske.