✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun tare hanya a Zamfara, sun kone matafiya 6 a cikin mota

Maharan sun kuma banka wa wasu motocin wuta da fasinjoji a ciki.

Akalla mutum shida ne aka kashe, wasu da dama kuma aka yi garkuwa da su bayan da ’yan bindiga suka tare hanyar Kauran Namoda zuwa Shinkafi a Jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa maharan sun kuma banka wa wasu daga cikin motocin da suka tare wuta da fasinjoji a ciki, kuma ko gawarwakinsu ba a iya ganewa.

A cewarsu, akasarin maharan, wadanda yaran kasurgumin dan bindigar nan ne da aka fi sani da Turji, sun zafafa kai hare-hare a yankin a cikin ’yan kwanakin nan, tun bayan da wani harin sojojin sama ya kashe masa wata gwaggo da mijinta da kuma mayakansa da dama.

“’Yan bindigar sun tare hanyar ce a daidai tsakanin Kwanar Jangeru da Moriki, wacce dama tuni matafiya suka daina bi saboda rashin tsaro. Babu wanda zai iya zuwa ma ya kwaso gawarwakin mutanen da aka kashe,” inji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa.

Shi kuwa wani mazaunin yankin mai suna Mansur cewa ya yi, “Ka san harin da sojojin sama suka kai kwanan nan ne ya fusata su. Harin ya ragargaza daya daga cikin sansanonin Turji, sannan ya kashe ’yan uwansa da yaransa da dama.”

To sai dai wasu majiyoyin sun ce ’yan bindigar sun dawo da kai hare-haren ne don su nuna bacin ransu da ci gaba da rufe kasuwar dabbobi ta garin Shinkafi.

An dai jiyo wasu daga cikinsu na cewa za su ci gaba da kai hare-hare a yankin har sai lokacin da aka sake bude kasuwar dabbobin.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’yan sandan Jihar, SP Muhammad Shehu ya ce a ba shi lokaci zai tuntuba daga bisani, ko da yake bai yi hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.