✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sako Shugaban Karamar Hukumar da suka sace a Nasarawa

An sako su ne bayan biyan kudin fansa

’Yan bindigar da suka sace Shugaban Karamar Hukumar Keffi da ke Jihar Nasarawa, Baba Shehu tare da direbansa, Tanimu (Senior Man) sun sako su.

Majiyarmu wacce ke da kusanci da wadanda lamarin ya shafa ta ce an sako su ne ranar Asabar da misalin karfe 12:00 na dare bayan biyan kudin fansa na Naira miliyan N10 da dubu 200.

Tuni dai suka iso gidajensu cikin koshin lafiya.

Yayin harin dai, maharan sun sace Shugaban Karamar Hukumar ne tare da harbe dogarinsa, Alhassan Habeeb, har lahira.

Shugaban Karamar Hukumar tare da direbansa
Shugaban Karamar Hukumar tare da direbansa

Lamarin ya faru ne ranar Juma’a da dare a hanyar Akwanga zuwa Gudi, a lokacin da suke kan hanyarsu ta komowa Keffi daga Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa.

Rahotanni daga jihar sun ce maharan sun kira suna neman a biya su Naira miliyan 30 kafin su sako Shugaban Karamar Hukumar Keffin tare da direbansa, Tanimu Senior Man da suke hannunsu.

A ’yan kwanakin nan dai rahotanni sun nuna masu garkuwa da mutane sun matsa wa hanyar Gudi zuwa Akwanga inda suka yawaita kai hare-hare a yankin.