✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun saki sabon bidiyon fasinjojin jirgin kasan da ke hannunsu

’Yan ta’adda sun saki sabon bidiyon fasinjojin da suka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

’Yan ta’adda sun saki sabon bidiyon fasinjojin da suka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

A sabon bidiyonsu da ’yan bingidar suka fitar, fasinojijin da aka nuna su takwas, maza biyar mata uku, sun roki Gwamnatin Tarayya ta biya wa ’yan bindigar bukatunsu.

An tare jirgin ne minti 20 kafin isarsa Kaduna bayan ya taso daga Abuja ranar 28 ga watan Maris, 2022.

Maharan suka kashe mutum tara, suka jikkata wasu, tare da sace wasu sama da 60, ciki har da kananan yara da tsofaffi da mata.

Daga baya ’yan bindigar suka fitar da bidiyon fasinjojin da ke hannunsu.

A daya daga bidiyon da ’yan bindigar suka fitar, sun yi barazanar kashe fasinjojin idan Gwamnatin Tarayya ba ta sako ’ya’yansu da wasu ’yan ta’adda da ke hannunta ba.

Daya daga cikin fasinjojin, Sadiq, dan dattijon Arewa, Farfesa  Ango Abdullahi, ya ce yawancin fasinjojin suna fama da rashin lafiya.

“Muna kara rokon Gwamnatin Tarayya ta kawo mana dauki, yanzu kwananmu 62  ke nan a wannan wurin. 

“Yawancinmu ba su da lafiya kuma kullum abin kara ta’azzara yake yi.

“Muna rokon gwamnati ta kawo mana dauki kafin mu fara rasa rayukanmu,” inji shi.

Daga cikin fasinjojin, wata wadda ta ce ajinsu daya da Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo a Makarantar Koyar Aikin Lauya, fashewa ta yi da kuka, cewa tana cikin tashin hankali kan halin da danta mai fama da cutar sikila yake ciki.

“Sunana Gladys… Suna kira musamman ga Yemi Osinbajo wanda ajinmu daya a  78/79 a ‘law school’. 

“Kai uba ne kuma kaka, ka taimaka ka kawo mana dauki, kwananmu 62 a nan, ga shi kuma dana sikila ne; Yanzu ban san halin da yake ciki ba.”

“Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da kuma Rotimi Amaechi, wanda shi ne Ministan Sufuri ka kawo mana dauki. Ina rokon ka, ba mu da lafiya.”