✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sake kone ofishin ’yan sanda a Imo

Maharan sun jefa ababen fashewa cikin ofishin 'yan sandan.

Wasu mahara sun kone ofishin ’yan sanda na yankin Afor Atta da ke Karamar Hukumar Njaba a Jihar Imo.

Wannan na zuwa sa’o’i 24 bayan wani hari da wasu ’yan-ina-da-kisa suka kai wa tsohon gwamnan jihar, Ikedi Ohakim.

Maharan sun jefa wasu ababen fashewa cikin ofishin ’yan sandan, lamarin da ya sanya ta kama da wuta.

A watan Yunin 2021 ma wasu bata-gari sun lalata wani sashe na wannan caji ofis tare da kone wasu kotu biyu da ke daura da ofishin ’yan sandan.

Sai dai ba a samu rahoton rauni a bangaren ’yan sanda a sakamakon harin da suka kai ba.

Jin ta bakin kakakin ‘yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, ya ci tura sakamakon wayarsa na kashe.