✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sake kashe wani Fasto a Edo

Rahotanni da ke fitowa sun nuna wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun halaka wani Fasto da ke Limanci…

Rahotanni da ke fitowa sun nuna wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun halaka wani Fasto da ke Limanci a Cocin Christ Chosen Church Of God da ke karamar Hukumar Egor na Jihar Edo.

Kamar yadda rahoton ya nuna, Fasto Benson Isibor ya rasu ne bayan maharansa sun yi masa kwanton-baunta inda suka bude masa wuta a lokacin da yake kokarin shiga gidansa da ke Layin Oranmiyan daura da Layin Siluko a daren Litinin da ta gabata.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Edo Johnson Babatunde Kokumo ya tabbatar wa da manema labarai aukuwar wannan lamari a ranar Talatar da ta wuce a lokacin da yake gabatar da wadansu bata-gari 28 da ake zargin sun aikata laifuffuka daban-daban kuma rundunarsa ta yi nasarar damke su.

Ya ce an kama bata-garin ne da laifuffukan da suka hada da na yin garkuwa da mutane da kungiyar matsafa da ta ’yan fashi da makami da kuma ta kisan kai.  Ya ce an samu nasarar kama su a yayin da suke aikata ta’asa a sassan jihar a lokuta daban-daban.

Da Kwamishinan ’yan sandan yake karin haske game da kisan gillar da aka yi wa FastoBenson Isobor, ya ce wasu mahara ne suka yi wa faston kwanton bauna kuma suka bude masa wuta a lokacin da yake kokarin shiga gidansa, inda ya mutu nan take.

“Wannan ya tabbatar da cewa wasu ne suka kashe faston da gangan a lokacin da yake kokarin shiga gidansa saboda bai yi zaton akwai wadanda suka dana masa tarko don su hallaka shi ba.”

Sai dai ya ce rundunarsa ta yi nasarar kama Tahir Usman da ake zargin yana da hannu a kashe wani Fasto Mista Pius Eromonsele Odighi a karamar Hukumar Obia ta Gabas da ke Jihar Edo a kwanakin baya.  “Wannan shi ne karo na biyu da aka kashe fastoci biyu a ’yan kwanakin nan a jihar Edo,” inji shi.

A kwanakin baya ne aka hallaka faston, kuma a binciken da rundunar ’yan sandan jihar ta yi game da batun ne ta samu nasarar cafke Tahir Usman, inji Kwamishinan ’yan sandan.

Kwamishinan ya kara da cewa rundunarsa ta yi nasarar kama Abubakar Iliyasu da ake zargin ya dade yana damun al’ummar Auchi da kewaye wajen yin garkuwa da mutane.  Sannan an kama wadansu masu garkuwa da mutane su biyu da suka yi sojan gona kamar  makiyaya a cikin dajin Afuze da ke karamar Hukumar Owan ta Gabas da ke jihar, inda yanzu haka ake ci gaba da bincike a kansu.

Ya ce dukkan wadanda aka kama sun tabbatar da aikata laifuffukan da ake zarginsu da shi a yayin da ake bincikarsu kuma da zarar rundunarsa ta kammala binciken za ta gabatar da su a gaban kotu don a yi musu hukuncin da ya dace da su.

Daga nan ya nemi al’ummar jihar su rika sanar da rundunarsa bayanan sirri game da bata-gari don a dauki matakin gaggawa a kansu.