Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kashe mutum 17 a wani sabon hari da suka kai a unguwar Magami da ke gundumar Faru a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
A cikin wannan watan na Disamba ‘yan fashi da makami sun kashe sama da mutum 50 a hare-haren da suke ta kaiwa unguwannin karkara a jihar.
Rahotanni na bayyana cewa, ko a ranar Laraba da ta gabata an kashe mutum 25 a harin da aka kai a kauyuka biyu wanda ake zargin ‘yan fashi ne da barayin shanu suka kai a karamar hukumar Birnin Magaji da ke jihar.