✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace ’yan sanda uku a Zamfara

Wasu ’yan bindiga sun sace ’yan sanda uku da ke aiki a ofishin ’yan sanda na garin Keta da ke Karamar Hukumar Tsafe a cikin…

Wasu ’yan bindiga sun sace ’yan sanda uku da ke aiki a ofishin ’yan sanda na garin Keta da ke Karamar Hukumar Tsafe a cikin jihar Zamfara.
Gomman ’yan bindigar wadanda ba a gano su ba, sun je kauyen inda suka kai hari ofishin ’yan sandan garin amma kuma ba a san dalilin kai harin ba.
Jihar Zamfara ta dan samu kwarya-kwaryar zaman lafiya bayan da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Mataimakin Gwamnan jihar, Ibrahim Wakkala Muhammad ya jagoranci yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin barayin shanu da ’yan sintiri a watan Disamban shekarar 2016.
Amma kuma ana ci gaban da samun kai hare-hare a wasu garuruwa wanda aka yi imanin wasu ’yan bindigar da ke yin barazana ga yarjejeniyar zaman lafiya suke kaiwa.