Wasu ’yan bindiga sun sace Sarkin Kajuru mai daraja ta biyu, Alhaji Alhassan Adamu a gidansa da ke Kajuru a Jihar Kaduna.
’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da iyalan basaraken guda 12, ciki har da mata da kananan yara.
- Mukabalar Kano: Za a gurfanar da Abduljabbar a gaban kotu
- APC ta dage manyan tarukanta har sai abin da hali ya yi
Jikan basaraken, kuma mai rike da sarautar Dan Kajuru a masarautar, Sa’idu Musa ne ya tabbatar da hakan ga Aminiya.
Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na daren ranar Asabar.
Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, da kakakin ’yan sandan Kaduna, Mohammed Jalige basu amsa kiran wayar da aka yi musu a kan lamarin ba.
Wannan dai shine hari na baya bayan nan daga cikin irin hare-haren da ake kai wa a Jihar ta Kaduna.
Ko da yake ’yan bindigar sun jima suna cin karensu ba babbaka a Jihar, amma a ’yan kwanakin nan abubuwa sun dada ta’azzara.