Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun sace mutum takwas a tsakanin garuruwan Okhuessan da Emu dake karamar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas a jihar Edo.
Wani wanda lamarin ya faru a kan idanunsa ya ce ‘yan bindigar sun fito ne daga cikin daji sannan suka tilastawa motar fasinjojin ta tsaya suka kwace duk kayan da suke tafe da su.
- Masu garkuwa da daliban ABU 9 na neman N270m a matsayin kudin fansa
- ’Yan bindiga sun sace ’yan sanda 12 a hanyar Zamfara-Katsina
Majiyar ta kuma ce mutanen na kan hanyarsu ne daga garin Ubiaja zuwa wurare daban-daban lokacin da maharan suka yi musu dirar mikiya.
A cewar majiyar, bayan sun raba matafiyan da kayayyakinsu, sai suka saki dukkan fasinjoji maza da kuma wasu mata tsofaffi, yayin da suka yi awon gaba da dukkan matan dake ciki zuwa daji.
Da muka tuntubi kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar, Chidi Nwabuzor ya ce har yanzu ba su sami rahoton faruwar lamarin ba.