✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace mutum 6 a Abuja

Mai garin Tungan-Maje ya koka kan yadda 'yan bindiga suka addabi garin.

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mutum shida a yankin Tungan-Maje da ke Gwagwalada a Abuja, babban birnin Najeriya.

Wani mazaunin yankin mai suna Yahaya, ya bayyana cewar lamarin ya faru da misalin karfe 11:46 na daren ranar Litinin, yayin da ’yan bindigar suka farmaki Unguwar Dabiri da Unguwar Sarki a yankin.

  1. An yi garkuwa da mahaifiyar Sakataren Gwamnatin Bayelsa
  2. Abale: Nas din da ya yi fice da dabanci a Kannywood

Ya ce ’yan bindigar sun kasu gida uku inda suka kai farmaki gidaje uku sannan suka yi awon gaba da mutane.

“Wasu daga ’yan bindigar sun tsaya a waje yayin da ragowar suka cikin gidajen suka yi awon gaba da mutane sannan suka tsere cikin daji da su,” inji Yahaya.

Mai garin Tungan-Maje, Alhaji Hussaini Barde ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma koka kan yadda ’yan bindiga suka addabi garin.

“Ayyukan ’yan bindiga a Tungan-Maje ya dade yana barazana ga zaman lafiyar jama’ata.

“Ina mai tabbatar da cewar tun daga Satumbar bara ’yan bindiga sun kawo munanan hare-hare guda 9,” a cewarsa.

Tungan-Maje, ya nemi masu ruwa da tsaki da su kawo wa yankin nasu dauki duba da yadda ake musu dauki dai-dai.

Sai dai neman jin ta bakin kakakin ’yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf ya ci tura, a yayin da ba ta amsa kiran wayarta ba ko mayar da sakon kar-ta-kwana da wakilinmu ya aike mata ba.

%d bloggers like this: