✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mutum 16 a Taraba

Lamari dai ya auku ne a ƙauyukan Dekko da Lama da Monkin da ke Karamar Hukumar Zing ta jihar.

Wasu gungun mahara ɗauke da manyan bindigogi sun sace mutum 16 a yayin wani hari da suka kai ƙauyukan uku a Jihar Taraba.

Wannan lamari dai ya auku ne a ƙauyukan Dekko da Lama da Monkin da ke Karamar Hukumar Zing ta jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa maharan waɗanda ake zargin sun haura mutum ɗari sun kai farmaki ƙauyukan uku ne da tsakiyar daren Juma’a.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, galibi mazauna ƙauyukan waɗanda suka tsallake rijiya da baya sun tsere saman tsaunukan da ke kewaye da su da rauni na harsashin bindiga.

Wata majiya ta ce ’yan bindigar na daga cikin ’yan ta’addan da sojoji da ’yan bijilanti suka fatattaka daga yankunan Karamar Hukumar Yorro ta jiha.

Kakakin rundunar ’yan sanda jihar, SP Usman Abdullahi ya tabbatar ta aukuwar lamarin, sai dai ya ce yana jiran karin bayani da kuma haƙiƙanin adadin mutanen da aka sace a ƙauyukan.