✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan bindiga sun sace mutum 10 a Abuja

Abun ya faru ne kan hanyar su ta dawowa Kuje bayan ziyarar da suka kai wani kauye a safiyar ranar.

A ranar Asabar ’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 10 a gudumar Kuje da ke birnin Tarayya, Abuja.

Daga cikin wadansa aka kama akwai Tsohon Mataimaki Shugaban gundumar wanda a yanzu haka shi ne Sarkin Noman Kuje.

Majiyar da ba da shaida ta ce, abun ya faru ne kan hanyar su ta dawowa Kuje bayan ziyarar da suka kai wani kauye a safiyar ranar.

Majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta ta ce, mutanen da aka sace ’yan unguwar Gade ne a gundumar ta Kuje.

Ta ce kuma har yanzu wadanda suka yi garkuwa da mutane ba su nemi kudin fansa ba.

Kawo yanzu ’yan sanda ba su ce komai kan tambayar da Aminiya ta yi musu kan lamarin ba, amma mai baiwa Shugaban Gundumar ta Kuje shawara, Sulaiman Sabo, ya tabbatar da faruwar lamarin.