Rundunar ’yan sandan Jihar Ekiti ta bayar da rahoton sace wani manomi a Karamar Hukumar Ikole da ke jihar.
Kakakin ’Yan sandan Jihar, ASP Sunday Abutu ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin ganawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar.
Ya ce, “Tabbas da Yammacin nan wani ya shigar da rahoton sace mutumin a caji ofis din Ikole wanda ya sanar cewa an sace mutumin ne a daren ranar Juma’a.
“Nan da nan muka bai wa jami’anmu cikakken bayanan mutumin kuma suka dukufa don ganin sun ceto shi,” a cewar Abutu.
Bayanai sun ce ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutumin mai suna, Alhaji Jimoh Olodan a lokacin da ya fita noma a wata gonarsa da ke wajen gari.
Wani jagoran al’umma a yankin, Cif Ajayi Ogungbemi, wanda ya tabbatar da faruwar hakan ya ce, ’yan bindigar da adadinsu ya kai 18 sun same mutumin a gona kuma suka tafi da shi ba tare da sun taba wani ba.
Sai dai ya bayyana cewa ’yan bindigar sun rika harbi a iska na tsawon wani lokaci domin razanar da mutane kafin daga bisani su kama gabansu.