✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace manoma 27 a hanyar Birnin Gwari

An yi awon gaba da su yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu.

Akalla manoma 27 ne ’yan bindiga suka sace a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne yayin da manoman ke kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu da misalin karfe 9:30 na safe a yankin Tsaunin Kunei da ke Karamar Hukumar Chikun ta jihar, a ranar Lahadi.

Aminiya ta gano cewa mutum tara daga cikin manoman mazauna kauyukan Udawa, Marinai da Damari na Jihar Kaduna ne, ragowar 18 kuma sun fito ne daga kauyukan Kusheka, Mashekari, Lukwape da Shiroro na Jihar Neja.

Shugaban yankin Udawa, Mohammed Umaru ya tabbatar da faruwar lamarin ga jami’an tsaro.

A cewarsa, har yanzu ’yan bindigar ba su tuntubi iyalan mutane da suka sace ba kan yadda za a yi kafin sakin su.

Ya bayyana cewa mazauna kauyukan da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari suna cikin firgici duk lokacin da za su je gonakinsu saboda tsoron za a iya sace su.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, kan faruwar lamarin, amma ba ya daukar waya kuma bai ba da amsar rubutaccen sakon da aka tura mishi ba.