✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace mahaifi da dansa a Abuja

Da jijjifin safiyar ranar Lahadi ’yan bindiga suk yi dirar mikiya a yankin Kuchiko na Karamar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja, inda…

Da jijjifin safiyar ranar Lahadi ’yan bindiga suk yi dirar mikiya a yankin Kuchiko na Karamar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja, inda suka yi awon gaba da wani mahaifi da dansa.

Aminiya ta gano cewa ’yan bindigar da yawansu ya kai fiye da 20 ne suka kai hari a unguwar da aka fi sani da Rukunin Gidajen El-Rufai da misalin karfe 12 na daren Lahadi; sun yi ta harbi kan mai tsautsayi.

Ko da masu gadin unguwar suka ci karfinsu, ’yan bindigar wadanda ke rike da wukake da arduna sai suka tasamma gidan mutum da suka sace inda suka yi awon gaba da shi tare da dansa.

Sauran mazauna unguwar sun samu kansu cikin zullumi wadanda karar harbin bindigogi ya sa suka farka.

Bayanai sun ce maharan sun shafe awa guda suna aika-aikarsu, daga bisani kuma suka nufi gidan wani mutum wanda shi ma suka yi yunkurin garkuwa da shi.

Koda yake, daukin da sojoji daga Kwalejin Tsaro ta Bwari suka kai kan lokaci ya taimaka gaya bayan musayar wutar da aka yi da ’yan bindigar.

Wasu mazauna unguwar wadanda suka bayyana halin da suka samu kansuy ciki sun yi kira ga mahukunta da su kara tsaurara tsaro a garuruwan da ke kewaye da Abuja.

Kokarin da Aminiya ta yin a jin ta bakin Babban Jami’in ’Yan Sandan Bwari ya ci tura, a daidai lokacin rubuta rahoton nan.