✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace Limami da iyalansa biyu a Kaduna

Ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani game lamarin.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani babban Limamin cocin Katolika tare da mai dakinsa da yaronsu a jihar Kaduna.

Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a yankin Dogon Kurmi da ke Karamar Hukumar Kagarko a jihar ta Kaduna.

Ya zuwa wannan lokaci na hada wannan rahoto, babu cikakken bayani game wanda suka yi garkuwa da su.

Sai dai wakilinmu ya tuntubi daya daga cikin Limaman cocin mai suna Rabaran Stephen Onyena, wanda ya ce an tabbas an sace malamin amma ba shi da cikakken bayani game da lamarin.

Yayin da wakilinmu ya nemi jin ta bakin wasu daga cikin manyan Limamai na wasu cocin da ke Kaduna, an yi rashin sa’a ba su amsa kiran wayarsu ba.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, ya ce rundunarsu ba ta samu labarin ba, amma za su fadada bincike don gano hakikanin abin da ya faru.