✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace daliban sakandire a Kaduna

Ba a san adadin daliban da suka sace ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun kai hari a kan wata makarantar sakandire mai suna Bethel Baptist High School a Jihar Kaduna.

Wakilinmu ya ruwaito cewa ’yan bindigar, wadanda suka kai hari da safiyar Litinin, sun sace dalibai da dama a sakandiren da ke Karamar Hukumar Chikun a Kudancin Kaduna.

Maharan sun fasa gini daga wani sashe na katangar makarantar ta mata da maza ta inda suka samu damar shiga suka kuma sulale da daliban.

Wani bidiyo da wakilinmu ya nada ya nuna yadda iyayen daliban maza ta mata da sauran jama’ar gari suka taru a bakin makarantar cikin zulumi.

Iyayen daliban sun kuma tare babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia domin nuna fushinsu a kan lamarin.

Yadda mutane suka taru a bakin makarantar
Wasu dga cikin iyayen daliban da suka tare hanyar Kaduna zuwa Kachia
Yadda wasu iyayen daliban da suka yi zaman dirshan a hanyar Kaduna zuwa Kachia
Wata uwa har da kwanciya domin nuna bacin rai kan satar daliban
Yadda dakunan kwanan daliban ya zama fayau
Ginin da maharan suka fasa a wani sashe na katangar makarantar

A wata hira da Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen Jihar Kaduna, Rabaran Joseph Hayab ya yi da sashen Hausa BBC, ya ce dansa na cikin daliban makarantar amma ya kubuta.

Duk da yake ba a san adadin daliban da aka sace ba, Rabaran Hayab ya ce “a ranar Juma’a mun kirga dalibai 180 da suka bangaren kwana, amma a safiyar nan yaran da muka samu ba su fi 24 zuwa 27 ba.”

Sai dai har yanzu hukumomi basu uffan ba dangane da lamarin.