’Yan bindiga sun kutsa wata Jami’ar Jarvis mai zaman kanta inda suka raunata dalibai da dama, suka kuma yi awon gaba da wani dalibi.
’Yan bindigar sun kai harin ne a Jami’ar Jarvis da ke Jihar Kuros Riba, a lokacin da daliban ke dawowa daga ajujuwansu bayan daukar darasi, a ranar Talata.
- Injin jirgin sama ya lalace yana tsaka da shawagi a Najeriya
- DAGA LARABA: Dalilan Da Daliban Kano Ke Yawan Faduwa Jarabawa
Daliban da suka tsallake rijiya da baya sun ce jiyo harbe-harbe wanda ya sa suka ari na kare, amma duk da haka sai da ’yan bindigar suka samu nasarar sace daya dag cikinsu, suka ruga da shi daji mafi kusa da su.
Jami’ar Jarvis da ke Karamar Hukumar Akabuyo ta Jihar Kuros Riba, mallakin wani dan siyasa da ya taba takarar gwamnan jihar.
Hukumar gudanarwar jami’ar ta tabbatar da kutsen da maharan suka yi ta cikin wata sanarwa, amma ta bukaci daliban da iyaye su kwantar da hankulansu, domin ta dauki matakan hana sake faruwar hakan.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kuros Riba, Irene Ugbo, ya ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan jihar ya tashi tawaga ta musamman domin tabbatar da bin doka a jam’iar, da kuma farauto wadanda suka sace dalibin.