’Yan sanda a Jihar Bauchi sun kama wasu da ake zargin da kashe dan majalisa mai wakiltar Dass, Musa Mante, shekaru biyu da suka gabata.
A watan Agustan 2020 ne dai aka sace Musa da matansa biyu tare da ’yarsa mai shekara daya, inda aka nemi kudin fansarsu N30m.
- Matar mai wakar ‘Najeriya Jaga-Jaga’ ta ba da kodarta an dasa masa
- NAJERIYA A YAU: Zaben 2023: Shin Zai Yiwu A Tura Sakamako Ta Intanet?
Da yake holen masu laifin, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ’yan ta’addan sun bai wa sashin binciken sirri na rundunar wahala kafin a kamo su, bayan ’yan samun rahoton sirri.
Kazalika a cewarsa, sun ci gaba da amfani da hikima da dabarun aiki tsawon shekaru biyu kafin su samu nasarar kamo su.
“Wadannan mutanen, sun amsa cewa su suka kashe Mante, suka kuma sace iyalinsa a watan Agustan 2020.
“Bayan haka kuma sun ce su suka kashe wani Babban Sifiritandan Dan Sanda mai ritaya mai suna CSP Garkuwa, saboda hana su rawar gaban hantsi da suka ce ya yi.
“Sai kuma wani Mallam Dahiru Suleiman, da shi ma suka ce sun kashe”, in ji Adejobi.
Wadanda ake zargin dai sun ce sun kashe Mante ne, bisa hana su kudi da yayi, duk rokon da suka yi masa.
Shugabansu ya ce sun haura gidan Mante ne da daddare, inda suka kashe shi, suka kuma sace kudi N2m a dakinsa.
Daga nan ne suka hada kan iyalinsa suka kai su wani guri wai shi Dutsin Miagoshi Igala, bayan kwana hudu suka bukaci N35m kudin fansa.
Kakakin ya ce za su maka su a kotu ne, bisa zargin su da aikata laifukan hadin baki wajen aikata babban laifi da kisan kai da kuma garkuwa da mutane.