’Yan bindiga sun yi garkuwa da wata amarya da ake dab da daura arenta tare da wasu mutun uku ’yan gida daya da wasu mutane kuma a Kaduna.
Aminiya ta gano maharan sun kutsa unguwar Rigachikun ne da misalin karfe 1 na daren ranar Laraba, suka shiga wasu gidaje uku suka yi awon gaba da mutane.
- NAJERIYA A YAU: Da Bazara Wa Sabuwar Tafiyar TNM Za Ta Yi Rawa?
- Aikin alherin Ambasada Gwani ya sosa wa al’ummar Agangaro rai
Wata dattijuwa da jikokinta uku ke cikin wadanda aka yi garkuwa da su a harin ta ce maharan sun kutsa dakin da su amaryar mai suna Khadija suke barci ne sannan suka tafi da su.
Ta ce, “Muna barci lokacin da suka shigo suka ce Khadija da Shu’aibu su taso su bi su. Sannan sun dauke wata waya da wani guntun burodi da ke kan tebur. Mun shiga tashin hankali.”
Basaraken unugwar, Idris Abdulrasheed, ya bayyana cewa karon farko ke nan da mahara suka kai hari a yankin, kuma tuni suka sanar da jami’an tsaro.
Ya bayyana cewa ’yan bindigar ba su tuntubi iyalan wadanda suka sace ba don neman kudin fansa.
Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, bai amsa wayar wakilinmu ba ballanta a ji ta bakinsa kan faruwar lamarin.