✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kone kotu kurmus a Imo

Maharan sun yi amfani da wasu ababen fashewa wajen kona kotun

Mahara sun kone wata kotun majistare a Owerri, babban birnin Jihar Imo, kasa da sa’a 24 da aka kai makamancinsa a wata babbar kotun jihar da ke yankin Orlu.

Wata majiya ta bayyana cewa maharan sun kai harin ne ta hanyar amfani da ababen fashewa kuma sun kone takardu da wasu muhimman abubuwa kurmus a kotun.

Wasu mazauna yankin da suka leka don gane wa idonsu yadda lamarin ya faru sun bayyana cewa maharan sun lalata kusan daukacin kotun.

Kakakin ’yan sandan Jihar Imo, Mike Abattam, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike don kamowa da kuma gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Kungiyar IPOB mai neman ballewa daga Najeriya dai ta zafafa kai hare-hare a kan cibiyoyin gwamnati a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya, musamman a Jihar Imo.

A baya-bayan nan hare-haren kungiyar sun yawaita a kan Ofisoshin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da kuma kotuna.

Rahoton INEC ya nuna sau tara aka kai wa ofisoshinta hari a Jihar Imo, baya ga wasu wurare a jimillar hare-hare 53 da aka kai wa cibiyoyin hukumar.