✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kona motocin matafiya 8 a Kaduna

’Yan bindiga sun cinna wa motoci akalla takwas wuta a kusa kauyen Manini da dajin Kurega forest kan babbar hayar Kaduna zuwa Birnin Gwari. Ana…

’Yan bindiga sun cinna wa motoci akalla takwas wuta a kusa kauyen Manini da dajin Kurega forest kan babbar hayar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Ana fargabar ’yan bindiga sun yi garkuwa da da dama daga cikin fasinjojin jering gwaon motocin da suka kai wa harin a safiyar Talata.

“Mun samu labari cewa an kona motoci takwas a ayarin motocin da ’yan ta’addan suka kai hari daga Manini zuwa Kurege a kan babbar hanyar; ana kuma fargabar cea sun yi awon gaba da mutane amma muna tsoron zuwa wurin da abin ya faru,’ inji wani mazaunin yankin.

Zuwa lokacin da muka samu labari babu cikakken bayani game da harin, amman wani mazaunin kauyen Kurega ya ce motoci takwas da aka kona sun hada da motocin haya da na kashin kai.
Sai dai dai ya bayyana wadansu daga cikin fasinjojin motocin sun samu sun tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukanu.

Ya ce, “Motocin na kan hanyarsu ta zuwa Kaduna aka tare su a wani wuri mai suna Tashar Ayuba kafin a kai tsakanin kurega da Manini.

“Ba mu san adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba, saboda ba wanda zai iya yin gangancin zuwa wurin ba tare da rakiya jami’an tsaro ba,” inji shi.

Kokarin wakilinmu na jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ya ci tura, bai samu amsa wayar wakilin namu ba.

%d bloggers like this: