✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda sun sace makamai

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda biyu da suka hada da wani Sufeto da Kurtu a harin da suka kai wani caji ofis a Karamar…

Yan bindiga sun kashe yan sanda biyu da suka hada da wani Sufeto da Kurtu a harin da suka kai wani caji ofis a Karamar Hukumar Igueben, Jihar Edo.

Maharan sun raunata ’yan sanda da dama, tare da sace makamai a ofishin bayan sun tarwatsa shi da nakiya.

Wata majiya ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:00 na dare, ranar Litinin inda maharan suka shiga rumbum makaman ‘yan sandan suka debe.

Rahotanni sun ce an kai gwarwakin ’yan sandan mucuware sannan matasa a garin sun yi zanga-zanga da  cewar maharani ba ’yan gari ne ba.

Masu zanga-zangar sun kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta yi binciken kan harin.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Edo, SP Chidi Nwabuzor, ya ce masa Kwamishin ’Yan Sanda zai yi jawabi kan abin da ya faru.