A ranar Alhamis din makon jiya ne da yamma wadansu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ko masu garkuwa da mutane ne suka hallaka wadansu ’yan sanda biyu a tsohon garin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, a wurin da ’yan sandan ke duba ababen hawa a kan titi.
’Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wadansu ’ya’yan kungiyar direbobi da ke Birnin Gwari a ranar, ciki har da Shugaban kungiyar Direbobi ta Birnin Gwari, Abdu Kano.
Wata majiya a garin da ba ta so a ambaci sunanta ba, ta bayyana wa Aminiya sunayen sauran wadanda aka sace da suka hada da Hamisu da Umar Ba-matsala da Safiyanu dandoka da Mika.
“Dukkansu mutanen Birnin Gwari ne kuma suna aiki ne a tashar Birnin Gwari, kuma suna hanyarsu ce ta dawowa daga garin Funtuwa inda suke ji bikin aure,” inji mijiyar.
Ta ce bayan da aka sace su ’yan bindigar sun bukaci a biya su fansar Naira miliyan hamsin.
Kuma Aminiya ta samu bayanin cewa iyalinsu sun yi tayin biyan Naira miliyan biyu da rabi ga masu garkuwa da su amma ba su amince ba.
Sai dai kuma a ranar Talatar nan sako shugabannin kungiyoyin direbobin bayan an biya diyyar Naira miliyan biyar.
Sakataren kungiyar Direbobi reshen Birnin Gwari, Almustapha Ahmad ya tabbatar wa Aminiya labarin sako mutanen, inda ya ce an sako su aka ajiye su kusa da tsohon garin Birnin Gwari.
“Yanzu haka suna tare da iyalinsu a gidajensu, sai dai muna kira ga gwamnati ta dauki mataki a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Funtua domin wadannan mutane na neman kashe hanyar,” inji shi.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna, Austin Iwar ya tabbatar da kashe ’yan sandan biyu sai dai bai yi karin bayani ba.