✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda biyu a Bauchi

An kashe ’yan sanda 10 a tsawon makonni biyun da suka gabata.

Wani Sufeton ’yan sanda, Mukhtar Ibrahim, ya yi gamo da ajalinsa yayin da wasu ’yan bindiga suka harbe shi a Jihar Bauchi.

’Yan bindiga sun bude wa rundunar ’yan sanda mai sintiri a kan manyan hanyoyi inda suka kashe Sufeta Ibrahim da wani abokin aikinsa a yankin Nabordo na Karamar Hukumar Toro ta Jihar.

Aminiya ta samu cewa abokin aikin nasa mai suna Uba Sama’ila, shi ne dan Dagacin garin Nabordo.

Kakakin rundunar ’yan sandan Bauchi, Ahmed Wakili wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne a daren ranar Asabar.

Ya ce Kwamishinan ’Yan sandan jihar, Abiodun Alabi, ya tura tawagar jami’an ’yan sanda su yi sintiri a yankin da lamarin ya auku.

Akalla jami’an ’yan sanda 10 aka kashe yayin da suke bakin aiki a tsawon makonni biyun da suka gabata.