✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 9 a Habasha

Harin ’yan bindigar yayi sanadin mutuwar 'yan sanda tara a Kudancin kasar.

Akalla ’yan sanda tara ne suka rasu a wani hari da ’yan bindiga suka kai Kudancin kasar Habasha a safiyar Talata.

Babban jami’in dan sandan yankin shiyyar Bench-Sheko, Dawit Timotiwos, ya tabbatar da mutuwar ’yan sandan.

Timotiwos, ya kara da cewa an samu karin jami’an ’yan sanda uku da suka ji rauni, amma bai bayyana ko su wane ne suka kai harin ba.

Sai dai ya ce jami’an tsaro na ci gaba da bincike don gurfanar da wanda suka yi sanadin mutuwar jami’an.

Rikicin kabilanci a kudancin Habasha ya yi kamari kuma ya dade yana sanadin asarar daruruwan rayuka da muhallai.

Rikicin kabilancin ya sami asali ne daga neman madafun iko da kuma albarkatun kasa.