✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe tsohon Kansila sun sace direbobin Dangote a Zariya

An kai harin ne a cikin dare yankin Dutsen Abba da ya yi kaurin suna da ayyukan masu garkuwa da mutane

’Yan bindiga sun kashe wani tsohon Kansila suka kuma yi awon gaba da direbobin kamfanin Dangote biyu da wasu mutum shida a kauyen Kugu da ke yankin Dutsen Abba a Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.

’Yan bindigar sun kutsa kauyen ne da misalin karfe daya na daren Juma’a suka farmaki kansilan, mai suna Usaman Ibrahim wanda akafi sani da Magaji, a gidansa amma ya haura ta katanga ya fita ta baya.

Fitarsa daga gidan domin tsira da ransa ke da wuya ne wasu daga cikin ’yan bindiga suka bude mishi wuta suka same shi a baya wanda hakan ya yi sanadiyar rasa ransa.

Bayanan da Aminiya ta samu sun nuna direbobin kamfanin Dangoten da lamarin ya ritsa da su ’yan unguwar ne, kuma abin ya ritsa da su ne a lokacin da suka dawo gida.

Wakilin Aminiya ya gano cewa an sallaci gawar tsohon Kansilan da aka kashe ne jim kadan bayan Sallar Juma’a.

Majiyarmu ta ce daga baya ’yan bindigar sun sako wasu mutum biyar daga cikin wadadanda maharan suka tafi da su.

Wasu majiyoyi a unguwar sun ce tun bayan lokacin da hukumomin tsaro suka sako wasu yaran unguwar da ake zargi da alaka da masu satar mutane don neman kudin fansa sha’anin tsaro a yankin ya tabarbare.