Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ‘yan bindiga sun kashe tsohon babban hafsan tsaron Najeriya Alex Badeh.
Kakakin rundunar sojin saman Najeriya Ibukunle Daramola ya sanar da hakan jiya Talata da daddare ya ce ‘yan bindigar sun kai hari kan motar da Badeh ke ciki lokacin da yake kan hanyar komawa gida daga gonarsa a kan titin Abuja zuwa Keffi.
Alex Badeh ya mutu ne bayan harbin bindigar da aka yi masa.