✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe mutum 9 a Kaduna

Akallam mutum tara ne ‘yan bindiga suka kashe a wani sabon hari da suka kai a Karamar Hukumar Kajuru ta jihar Kaduna. A safiyar Laraba…

Akallam mutum tara ne ‘yan bindiga suka kashe a wani sabon hari da suka kai a Karamar Hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

A safiyar Laraba ne maharan suka kai wa kauyen Tudu da ke Agwala Dutse hari tare da jikkata wasu da dama.

Shaidu sun tabbatar wa Aminiya cewa maharan dauke da bindigogi sun kutsa kauyen ne da misalin 5:00 inda suka tashi mazauna da harbe-harbe.

Shugaban Karamar Hukumar Kajuru Cafra Caino ya tabbatar a shafukansa na zumunta cewa mutane tara sun rasu a harin.

Caino ya ce harin babban koma baya ne ga kokarin da majalisar karamar hukumar ke yi na samar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da bangarorin manoma da makiyaya a yankin.

“Aikin samar da zaman lafiya ya rataya ne a wuyan kowa. A matsayinmu na karamar hukuma za mu dage da kokarin shawo kan wannan lamari da ya ki ci, ya ki cinyewa.

“Mu kadai ba za mu iya ba sai kowa a yankin ya ba da gudummawa,” inji shi.

Zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Kaduna ba ta ce komai game da harin ba.

Yankin karamar hukumar Kajuru da ke yankin Kaduna ta Tsakiya, amma take iyaka da karamar hukumar Kachia da ke kudancin Kaduna ta Kudancinta, na yawan fuskantar tashe-tashen hankula.

Kusan kowane mako sai an samu rahoton kai hari a yankin. Na karshe kafin wannan shi ne wanda wasu mahara a ranar Jumma’ar da ta gabata suka kai a yankin Agwala inda suka kona rugar Fulani, sai dai babu asarar rai a ciki.