’Yan bindiga sun hallaka kimanin mutun takwas, suka kuma yi awon gaba da wasu 28 a wasu munanan hare-hare a Kananan Hukumomin Kajuru da Kachia a Jihar Kaduna.
Shaidun gani da ido sun ce mutum tara ne aka bindige har lahira aka kuma yi awon gaba da wasu 28 a harin da ’yan bindigar suka kai a safiyar Talata.
- An kammala daukar shirin Labarina zango na uku
- Watan Azumi: Za a rage farashin kayan abinci da kashi 75
- Dan wasan Real Madrid, Rafael Varane ya kamu da COVID-19
- Sojoji na samun nasara a yaki da Boko Haram —Zulum
’Yan bindigar da suka tare hanyar Kaduna zuwa Kaduna kusa da Kasuwar Magani da kuma ta bangaren Doka a Karamar Hukumar Kachia sun bude wuata ne a kan wata bas, motar ice da kuma wata babbar mota.
Harin na safiayr Talata naauku ne washegarin da aka kubutar biyar daga cikin dalibai 39 da aka yi garkuwa da su a Kwalejin Gwandun Daji ta Tarayya da ke garin Kaduna, kwana 26 da suka gabata.
Sai dai da take sanar da harin, Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce rahoton da ta samu daga sojoji ya nuna mutum shida ne ’yan bindigar suka kashe, suka kuma jikkata wasu uku, amma ba ta ce uffan ba game da ko akwai wadanda aka yi garkuwa da su ba.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ya kara da cewa ’yan bindigar sun sace shanu 180 a wata rugar Fulani da ke kauyen Inlowo, bayan sun kashe wani mai suna Ibrahim Alhaji Haruna.
Ya ce a halin yanzu jami’an na ci gaba da gudanar da sintiri a yankin da nufin cafke wadanda suka yi barnar.
’Yan bindiga sun koma hanyar Kaduna-Kachia
Majiyoyin Aminiya daga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, sun ce ’yan bindiga sun koma kan hanyar Kachia zuwa Kaduna tun bayan da aka tsaurar matakan tsaro a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Sun ce tun wata Janairu ’yan bindiga suke addabar hanyar inda suke kai wa matafiya hari babu kakkautawa.