’Yan bindiga sun kashe mutum takwas tare da kona wani coci da ma gidaje da dama a Jihar Kaduna.
’Yan bindiga sun kai harin ne a Ungwan Gaida, daura da Kurmin Kaso, a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar, a cewar Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan.
- Likitoci sun ba El-Rufai awa 48 ya nemi afuwar ma’aikatan jinyan da ya kora
- ’Yan bindiga sun kai harin farko a garin Batsari
Aruwan ya kada da cewa jami’an sojin ruwa na Najeriya da aka girke a yankin Kujama sun kashe ’yan bindiga uku suka kuma kame wasu abokansu biyu bayan dakile wanin hari ’yan ta’addan a unguwar Wakwodna da ke yankin.
A cewarsa, bayan samun rahoton kai hari a Wakwodna, sojojin da aka a girke a wani shingen bincike a Kujama sun kai dauki suka kuma fatattaki miyagun.
Ya ce ’yan fashin sun gudu zuwa cikin dajin da ke kusa, a lokacin da suka ga sojojin, suka kuma saki wasu shanun da suka sace, wadanda daga bisani aka mayar wa masu su.
Aruwan ya ce sojojin sun fafata da ’yan ta’addan ne a kauyen Kaso, kuma a yayin artabun, sun kashe ’yan binidiga guda uku.