✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kashe mutum 8 a Binuwai

Maharan sun fille kawunan wasu mutane da suka kashe sannan suka yi awon gaba da su.

Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari wani yanki daura da sansanin ‘yan gudun hijira da ke Abagena a Karamar Hukumar Makurdi ta Jihar Binuwai, sun kashe mutane takwas ciki har da kananan yara.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa wasu mutane takwas sun samu munanan raunuka kuma an kai su asibiti domin ba su agaji.

“Maharan sun fille kawunan wasu daga cikin wadanda suka kashe, sannan suka tafi da kawunan.

“Wani mutum da matarsa ​​da ’ya’yansa hudu duk sun mutu a harin.

“Watakila adadin mutanen da suka mutu ya karu saboda akwai wasu mutum uku da suka ji mummunan rauni kuma babu tabbacin za su rayu,” in ji majiyar.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Sewuese Anene, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya kara da cewa har yanzu ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba.

Anene ya ce ‘yan sanda sun baza jami’ansu domin takaita lamarin.