Haren-haren, wanda ake zargi wasu ‘yan bingida ne suka kai, ya auku ne a ranakun Lahadi da kuma Litinin da suka gabata kamar yadda BBC ta ruwaito.
A daidai wannan lokaci da ake zaman xarxar, gwamnan jihar ya sanya dokar taqaita zirga-zirga a yankin daga qarfe shida na safe zuwa shida na yamma bayan an tura jami’an tsaro domin su shawo kan lamarin, kamar yadda Daraktan yaxa labarai na gwamnan, Mista Emmanuel Nanle ya sanar, inda ya ce hakan ya zama tilas ne saboda “Yawan kai hare-haren da ake yi a yankin.”
Hakanan kuma. Rahotanni da ke fitowa daga jihar sun nuna cewa manyan jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki na jihar suna tattauna a kan yadda za su shawo lamarin.
Jihar Filato dai ta daxe tana fama da tashe tashen hankula waxanda ke da nasaba da qabilanci da addini a shekarun baya. Sai dai kuma an samu kwanciyar hankali a ‘yan kwanakin baya, kafin wannan rikicin ya sake varkewa.