‘Yan bindiga sun kashe mutum biyu a mazabar Kerawa da ke Karamar Hukumar Ighabi a jihar Kaduna.
Harin ya zo ne awanni 48 bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe wani mutum tare da raunata mutum biyu, ciki har da jami’in dan sanda a garin Kuyello da ke karamar hukumar Birnin Gwari.
- Kwastam ta kwace kayan N40m a Kaduna
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a Kaduna
- Barayi sun fasa ofishin Media Trust dake Kaduna
- Jami’an tsaro sun ceto mutane 4, sun cafke ‘yan bindiga 3 a Kaduna
Kwamishinan Tsaron Cikin Gida Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Mista Aruwan ya ce binciken da aka gudanar ya gano ‘yan bindigar sun kai harin ne gidan wani mutum da ke rugar Fulani inda suka yi wa yankin kawanya.
A sakamakon harin ne ‘yan bindigar suka harbe Alhaji Maikudu Husaini, yayin dan uwansa Nafiu Husaini, ya tsallake rijiya da baya da rauni na harbin bindiga.
Kwamishinan ya ce gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufai, ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wanda suka rasun.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, ‘yan bindiga sun kai farmaki yankunan ungwar Najaja, Anaba, Zangon Wada da Kamacha wadanda duk suke karkashin mazabar Kerawa da ke Jihar.