✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe manoma 2 suna shuka a gonarsu

Ko a bara ma an ce da kyar mahaifinsu ya sha a gonar

Wasu da ake zaton ’yan fashin daji ne sun harbe wasu samari biyu a lokacin da suke shuka a gonarsu da ke yankin Iyatawa a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Lamarin, wanda ya faru rana r Talata, ya jefa tsoro a zukatan manoma a yakin Zariya, a daidai lokacin da suka himmatu wajan aikata gonakinsu saboda saukar ruwan sama.

Mutanen da lamarin ya ritsa da su dai, Alhaji Mustapha Lawal da Bello Lawal wa da kani ne, kuma mazauna unguwar Kofar Jatau da ke cikin Zariya.

Bayanan da Aminiya ta samu sun nuna ko a daminar bara, mahaifinsu yasha da kyar a lokacin da ’yan bindigar suka raunata shi da sara da suka inda ya yi jinya matuka.

Manoman da Aminiya ta zanta da su, sunyi bayanin, cewar baya ga rashin tsaro kuma suna fuskantar tsadar yanayin rayuwa, da tsadar takin zamani da duk wani kaya da ya shafi aikin gona.

Akan haka sun ce maganar noma a bana sai abin da Allah ya yi, amma suna rokon Allah mafita.